28 Yuli 2021 - 14:55
An Kama Wasu ‘Yan Ta’adda Masu Aiki Wa Кungiyar MOSSAD Ta Isra’ila A Iran

Ma’aikatar leƙen asiri da tattaro bayanan sirri ta Iran ta sanar da kame wasu gungun mutane da suke aiki wa ƙungiyar leƙen asirin haramtacciyar ƙasar Isra’ila MOSSAD tare da wani adadi mai yawa na makamai a kan iyakan ƙasar Iran ɗin ta yamma a ƙoƙarin da suke yi na haifar da fitina da gudanar da ayyukan ta’addanci.

ABNA24 : Yayin da ya ke sanar da hakan babban daraktan faɗa da ayyukan leƙen asiri na ma’aikatar ya ce an kama ‘yan amshin shatan ƙungiyar ta MOSSAD ne lokacin da suka shigo Iran ta kan iyakan ƙasar ta yamma biyo bayan gagarumin aikin sanya ido da jami’an ma’aikatar suka jima suna yi.

Jami’in dai bai yi ƙarin bayani kan haƙiƙanin inda aka kama mutanen da kuma adadinsu ba, sai dai ya ce mutanen suna shirin amfani da waɗannan makaman ne wajen tayar da fitina da kuma kashe wasu mutane a cikin Iran ɗin.

Daga baya dai ma’aikatar ta nuna wani faifan bidiyo na kaɗan daga cikin ayyukan sanya ido kan mutanen da yadda aka kama su bugu da ƙari kan nau’oin makaman da aka samu a tattare da su.

Makaman da aka samu ɗin dai sun haɗa da ƙananan bindigogi (pistol), gurneti-gurneti, manyan bindigogi na Kalashnikov, albarusai masu yawa da dai sauransu.

A baya ma dai masu aiki wa ƙungiyar ta MOSSAD sun so tada fitina a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a Iran a watan Yunin da ya gabata, sai dai kuma jami’an tsaron sun yi maganinsu da kuma kama wasu daga cikinsu.

342/